ABNA24 : Ministan harkokin wajen na Iran ya bayyana hakan ne cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter inda ya ce: Zin mutumcin musulmi biliyan 1.9 da kuma abubuwan da suke tsarkakewa saboda ayyukan da wasu masu tsaurin ra’ayin suka aikata, yin karen tsaye ne da batun ‘yancin fadin albarkacin baki, wanda kuma ba abin da zai haifar in ban da tsaurin ra’ayin.
Wadannan kalamai na ministan harkokin wajen na Iran suna zuwa ne a matsayin mayar da martani da kuma jan kunnen ga gwamnatin kasar Faransa musamman shugaban kasar Emmanuel Macron wanda cikin ‘yan makonnin ne ya zare wukar cin zarafin musulmi da musulmi da bayyana musulmin a matsayin ‘yan ta’adda kana kuma addinin Musulunci a matsayin addinin da ke cikin tsaka mai wuya a duniya, lamarin da ya ke ci gaba da fuskantar tofin Allah tsine daga bangarori daban-daban na duniyar musulmi.
342/